MENENE RIBAR DEMOKRADIYAR MU A ZURU EMIRATE AWANAN KARNI NA SIYASA TUN DAGA SHEKARAR 1999 ZUWA YAU?.
DAGA SALISU MUHAMMAD BALA
![](https://substackcdn.com/image/fetch/w_1456,c_limit,f_auto,q_auto:good,fl_progressive:steep/https%3A%2F%2Fbucketeer-e05bbc84-baa3-437e-9518-adb32be77984.s3.amazonaws.com%2Fpublic%2Fimages%2Fc087c3ee-3f01-4855-a115-a8236eb94704_1080x607.jpeg)
Tun 1999 da akafara siyasa awannan karnin, kasar zuru emirate take bada gudunmawarta awajen cigaban jaharmu ta kebbi state ta fanni dabam dabam,musaman ma ta bangaren siyasa.
Kowace jam'iyya (party) dake son kafa gwamnati sai ta nemi goyon baya da kuri'un mutanen kasar zuru emirate awajen tsaida dantakara, har zuwa wajen zaben gamegari a jiha amma anbaryaki baya ta fannin cin romo dimokradiyya bisa la'akari da duk muhimman ayuka/bukatoci (basic needs) na more rayuwar mutane ba'asamesu yada yakamataba.
Misalin wadannan ayuka sune kamar haka:
1.gyaran manyan hanyoyinmu na gwabnati tarayya.
2. Karkare permanent site na FSTC Zuru.
3. Samarda tashar gidan TV da NTA a zuru.
A jihar kebbi, zuru emirate tafi hanyoyi da aka fara aka fita batunsu ba'a kammala suba (abundant Road constructions).
Shawarwari akan Ayuka.
1 gyaran babbar titin koko zuwa zuru.
2 Karkare hanyar bajida. 3 hayar matseri da fashin garin Mahuta, fakai LG. 4 karkare hanyar sanchi,ushe da tadurga zuru LG. 5.karkare hanyoyin dan umaru, Ayu da fasa garin Ribah D/wasagu LG. 6 Yin hanyar diri zuwa makuku da sauran ayuka fasagari a sakaba LG.
A bangaren, ilimi akwai bukatar gyare gyaren makaratun kwana na secondary schools a yankin zuru emirate.
A bangaren Lafiya kananan dakunan shan magani na ward ward na bukatar gyara, inda babusu agina sabbi. Manya manyan asibitotanmu nason gyara da ingantawa, domi kulum Sai ankai marasa lafiyan mu birnin kebbi ko sokoto.
A bangaren Ruwan sha, akwai bukatar a yashe dam din zuru da yin kananan dam a sauran local governments, haka kuma anada bukatar water articulatio a sasa dabam dabam na zuru emirate.
Har ilayau, Zuru Emirate nada bukatar a gina kannan madatsun ruwa don manoman rani a wannan yanki.
Tafarnin Wutar Lantarki, akwai bukatar a inganta wuta kamar haka:
1 A kara inganta layin wutar Zuru zuwa birnin yauri.
2 Ana bukatar canza tiransfomomi, itatuwan wuta da sauran kaya don inganta wutar lantarki a emirate.
Sai batun tsaro, akwai bukatar tsaro a zuru Emirate muasaman yakin gabaci domin yanzu haka an fara samun barazana akan noma.
Bisa la'akari da wadannan matsaloli da bukatocin zuru emirate, munakira ga shuwagabani da wakilan kasar zuru emirate hadi da gwamnatin jihar kebbi, a duba wadanan matsaloli na zuru emirate.
SALISU BALA MUHAMMAD (S.A)
CHAIRMAN, ZURU EMIRATE YOUTHS IN POLITICS.
HAPPY DEMOCRACY DAY.